Home Labarai Wata mata yar shekara 29 ta rasa ranta sanadiyar zubar da ciki

Wata mata yar shekara 29 ta rasa ranta sanadiyar zubar da ciki

62
0

Rahama Ibrahim Turare/Banye

 

Wata mata mai suna Mrs.Chinesa Odah a jihar Ebonyi ta rasa ranta sakamakon shan ƙwayoyin zubar da ciki.

Matar wadda ake zargin tana satar ƙafa ta je wurin saurayinta Monday Mgbada ɗan shekara 25, wanda ake zargin ya yi mata cikin ya kuma bata ƙwayoyin zubar da cikin .

Mrs.Chinesa Odah, wadda take da ƴaƴa 4 ƴar asalin Inikiri Effun, dake ƙaramar hukumar Ohaukwu ta jihar Ebonyi, ta rasa ranta ne ranar 24 ga watan Agusta 2019 bayan ta sha ƙwayoyin.

Shedun gani da ido sun shedawa jaridar City Round cewa matar tafara zubda jini ne ,Inda mijinta Michael Odah, ya yi gaggwar kai ta asibitin Sudan Hospital da ke yankin, inda likitan dake bakin aiki ya tabbatar ma shi da cewa tasha wasu ƙwayoyi ne waɗanda suka lalata mata mahaifa .

Andai kai rahoton wannan lamarin a ofishin ƴan sanda na Effuim, inda take yanke aka kamo wanda ake zargin.

Chinesa wadda ke ta zubar da jini tayi bayanin cewa wani ne wai shi Monday Mgbada yayi mata cikin, kuma ya bata wasu ƙwayoyi ta sha don ta zubar da cikin, tana gama yin wannan bayanin sai rai yayi halin sa kamar yadda jaridar ta ruwaito .

Jami’ar yaɗa labarai ta rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah, ta tabbatar da mutuwar ta, kuma ta ce ana ci gaba da bincike akan faruwar lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply