Home Sabon Labari Wata rana dole za a kore ni daga Arsenal – Arteta

Wata rana dole za a kore ni daga Arsenal – Arteta

68
0

Mai horaswar Arsenal Mikel Arteta ya ce ƙungiyar na cikin mawuyacin hali, saidai ya ce bai jin tsoron ko ƙungiyar za su iya korarsa.

Wannan dai shi ne karon farko a cikin shekaru 39 da Arsenal ta kasa yin kataɓus a farkon kakar firimiyar Ingila, inda take mataki na 14 da maki 13 kacal.

Da yake magana bayan kashin da Gunners ta sha a gida hannun Wolves da ci 1-2, Arteta ya ce shi dama tun farkon zuwansa Arsenal ya sanya a ransa wata rana za a kore shi, saidai bai sani ba a farkon zuwansa ne ko kuwa zai yi ƙarko a ƙungiyar, amma dai wannan abu ne da ya ce ya zama dole ya faru.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply