Home Labarai Wata uwa ta kashe jaririn da ta haifa a Jigawa

Wata uwa ta kashe jaririn da ta haifa a Jigawa

84
0

Abdullahi Garba Jani

Yansanda a jihar Jigawa sun kama wata mata mai shekaru 18 da ake zargi da kashe jaririnta dan kwana daya da haihuwa bayan da aka tono gawar jaririn a karamar hukumar Ringim jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan jihar Abdul Jinjiri ne ya tabbatar da faruwar wannan lamarin a birnin Dutse.

Jinjiri ya ce an kama wadda ake zargin da ke da zama a kauyen Dandabi bisa zargin hada kai da kishiyar mamarta suka rufe gawar jinjirin wanda ta haifa ba ta hanyar aure ba.

Mai magana da yawun rundunar yansandan ya ce sun samu rahoto daga karamar hukumar Ringim cewa wata mata ta haifi jinjiri, amma dai ba a nan inda aka kai shi ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply