Home Sabon Labari Wenger na zawarcin komawa Arsenal

Wenger na zawarcin komawa Arsenal

102
0

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya bayyana cewa a shirye yake don komawa tsohuwar kungiyarsa ta Arsenal, sai dai ya ce ba lallai hakan ta yiwu ba.

Kocin ɗan ƙasar Faransa yana aiki da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, kuma shi ne kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tun daga shekarar 1996 zuwa 2018.

Tun bayan barin sa Arsenal kungiyar ke shan gwagwarmaya karkashin jagorancin koci Unai Emery da kuna Mikel Arteta da ke jagorantar kungiyar a yanzu.

Duk da kungiyar ce ta 13 a gasar Firimiya Arteta na cikin matsin lamba duk da nasarar da ya samu a wasansu da Chelsea da Brighton a ƙarshen shekara.

Wenger ya ce “Ashirye nike na taimake su madamar suka nemeni, amma bana zaton za su yi hakan”.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply