Home Coronavirus WHO ta ki amincewa da maganin gargajiya wajen warkar da COVID-19

WHO ta ki amincewa da maganin gargajiya wajen warkar da COVID-19

211
0

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta shawarci gwamnatoci da su tabbatar da ingancin maganin gargajiyar da Shugaban Kasar Madagascar Andry Rajoelina ya tallata a matsayin maganin cutar coronavirus.

Rajoelina na fatan raba maganin a yankin Yammacin Afirka da sauran kasashe, yana mai cewa maganin na kawar da Covid-19 a cikin kwana 10.

Tuni dai kasashen Equatorial Guinea, Guinea-Bissau, da jamhuriyar Nijar suka karbi wani kaso na maganin, yayin da kasar Tanzania ta nuna bukatar ta.

Sai dai kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta sha gargadin cewa babu wani binciken kimiyya a kan maganin samfarin ganyen shayi, kuma ba a yi gwajin karfin aikin shi ba a kimiyance.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply