Home Coronavirus WHO ta ziyarci Wuhan don gano asalin corona

WHO ta ziyarci Wuhan don gano asalin corona

30
0

Tawagar kwararru karkashin jagorancin hukumar lafiya ta duniya WHO ta sauka kasar China a garin Wuhan don bincike kan asalin cutar corona.

Wani jami’i a cikin tawagar ya bayyana, cewa an yi wa tawagar kwararrun gwajin na corona jim kadan bayan saukarsu, kuma an killace su na tsawon makonni 2 kafin su kama aiki.

Kwararrun za su yi aiki da jami’an kimiyya na kasar China don gano asalin bayyanar cutar ta corona.

Binciken ya biyo bayan zargin da kasar ta China ke yi kan cewa an shigo masu da cutar daga kasashen ketare ta hanyar daskararrun abinci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply