Home Labarai WTO: Gwamnonin Nijeriya sun taya Okonjo-Iweala murna

WTO: Gwamnonin Nijeriya sun taya Okonjo-Iweala murna

18
0

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, ta taya Dr. Ngozi Okonjo Iweala, murnar zabenta da aka yi a matsayin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya.

A wata sanarwa da ta fito daga jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Abdulrazaque Bello Barkindo, ya ce tabbatar tsohuwar Ministar kan wannan matsayi, abu ne da aka dade ana jira, kuma abu ne wanda ya cancanta.

Ya ce Dr. Ngozi Okonjo Iweala sanannniya ce a duniya a bangaren sanin tattalin arzikin, da ta yi aiki a manyan ma’aikatun kudi na duniya.

Ya kara da cewa, shekarun da ta yi a matsayin Ministar kudi ya sanya duniya ke yi mata kyakkywar fata na kawo sauyi ga kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta tsawon lokacin da za ta yi tana shugabancin kungiyar.

Kungiyar gwamnonin ta yi wa Okonjo-Iweala fatan alkhairi ga aikin da za ta fara daga ranar daya ga watan Maris, zuwa watan Agustan shekarar 2025.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply