Home Sabon Labari Xavi ya magantu kan yiwuwar komawarsa Barcelona

Xavi ya magantu kan yiwuwar komawarsa Barcelona

29
0

Mai horaswar kungiyar Al Sadd Xavi Hernandez ya ce dawowa ƙungiyar Barcelona, na ɗaya daga cikin abubuwan da suka daɗe a ran sa.

Akwai hasashe da yawa da ake yi na cewa Ronald Koeman ba zai ci gaba da zama a ƙungiyar ta Barca ba musamman duba da rashin nasarar da suka yi hannun PSG da ci 4-1 a wasan zakarun Turai na makon nan.

Ana ganin dai ba llai ba ne Koeman ya ci gaba da zama ƙungiyar, musamman yanzu da ake dab da yin zaɓen shugaban ƙungiyar, yayin da ake kyautata zaton Xavi ne zai maye gurbinsa.

Saidai kuma Xavi wanda ya shafe shekara 17 a Barcelona lokacin da yake taka leda, ya shaida wa shafin intanet na FIFA cewa yana jin daɗin inda yake, da rawar da yake taka wa a ƙungiyar Al Sadd ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi a yankin Asia.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply