Home Labarai Yaƙi da cin hanci: Martanin Buhari ga rahoton Transparency International

Yaƙi da cin hanci: Martanin Buhari ga rahoton Transparency International

33
0

Fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnatin shugaba Buhari ta cancanci yabo kan ƙoƙarin da take na yaƙi da cin hanci a ofisoshin gwamnati, kuma za ta ci gaba da goyon bayan hanawa, da ilmantar da jama’a kan illar ayyukan cin hanci a hukumomin gwamnatin.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Malam Garba Shehu ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a matsayin martani ga rahoton ƙungiyar Transparency International kan matsayin cin hanci a Nijeriya.

Rahoton dai ya ce Nijeriya ce ta 149 cikin ƙasashe 180 da suka fi fama da matsalar cin hanci a duniya, kuma ta 2 a yankin Afirka ta Yamma da maki 25 cikin 100.

Saidai kuma mai magana da yawun shugaban ƙasar ya yi watsi da rahoton tare da sa alamar tambaya ga hanyoyin da ƙungiyar ke tattare bayananta, yana mai cewa bayanan rahoton ba su yi daidai da haƙiƙanin abun da ke faruwa a ƙasar ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply