Home Labarai Yaƙi da Covid-19: Majalisar dokokin Kano za ta haɗa hannu da masarauta

Yaƙi da Covid-19: Majalisar dokokin Kano za ta haɗa hannu da masarauta

34
0

An yi Kira ga al’ummar jihar Kano su kasance masu biyayya ga matakan kariya daga cutar Covid-19.

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya yi wannan kira, lokacin da ya jagoranci wata tawaga daga majalisar zuwa Masarautar Kano a ranar Laraba.

Chidari ya ce sun kawo ziyarar ne domin haɗa hannu da masarautar wajen yakar cutar Covid-19 da ta yi kome karo na biyu.

A nasa jawabin mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna godiyarsa bisa wannan ziyarar, inda ya ce masarautar Kano kullum kofar ta abude take wajen karbar al’amuran da za su kawo ci gaba a fadin jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply