Home Coronavirus Yaƙi da Covid-19 na samun nasara a Sokoto bayan 75 sun warke

Yaƙi da Covid-19 na samun nasara a Sokoto bayan 75 sun warke

168
0

A jihar Sokoto, an sallami mutum 75 da suka warke daga cutar Covid-19.

Kwamitin kula da masu cutar Covid-19 na jihar ne, ya sanar da sallamar mutanen, inda adadin waɗanda suka warke daga cutar ya kai 113.

Kwamitin ya kuma tabbatar da cewa ba a samu wani mai ɗauke da cutar ba a cikin mutum 396 da aka keɓe, yayin da ake jiran sakamakon wasu mutum 10.

Mutum uku ne dai suka mutu sakamakon cutar a jihar Sokoto, duk da cewa dai an tabbatar suna ɗauke da wasu cutuka, da suka haɗa da ciwon suga, hawan jini da ciwon ƙoda.

Shugaban kwamitin yaki da cutar ta Covid-19 kuma kwamishinan lafiyan jihar Dr. Muhammad Ali Inname, ya alaƙanta wannan nasara da aka samu ga matakan da aka ɗauka na keɓance waɗanda ake zargi, yin gwaje-gwaje da kuma kula da waɗanda aka tabbatar sun kamu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply