Home Lafiya Yaƙi da shan Sigari: Ƙungiyoyi sun buƙaci ƙara haraji

Yaƙi da shan Sigari: Ƙungiyoyi sun buƙaci ƙara haraji

156
0

Hannatu Mani Abu/Banye

Masu rajin yaƙi da shan taba sigari a Nijeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara harajin da take karɓa daga masu kamfanin tabar sigarin domin ware wani kaso daga kuɗin wajen daƙile dabi’ar shan taba a kasar.

An yi wannan kiran ne a wani taron manema labaru da masu yaƙi da shan tabar sigari haɗin gwiwa da sauran kungiyoyi masu rajin hana sha da fataucin taba sigari a Nijeriya suka gudanar a Abuja.

Ƙungiyoyin dai sun bayyana cewa ƙara kuɗin harajin ga kamfanonin tabar sigari tare da ware wani kaso daga cikin kuɗin zai taimaka wajen yaƙi da kuma daƙile amfani da tabar a Nijeriya.

Hukumar lafiya ta duniya a wani rahoto da ta fitar ta bayyana cewa tabar sigari na hallaka aƙalla rabi daga cikin mashayanta, inda fiye da mutane miliyan takwas (8 million) ke mutuwa a kowace shekara sakamakon tu’ammali da taba sigari.

Bincike ya nuna cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da ke karɓar haraji mafi ƙaranci daga kamfanonin tabar.

Jaridar Premium Times wace ta bayar da wannan rahoto ta ce Akinbode oluwafemi ɗaya ne daga cikin masu ruwa da tsaki na ƙungiyar ya ce suna kira ga sabbin ministocin da aka naɗa musamman na ɓangaren lafiya da su kafa dokar da za ta taƙaita amfani da taba sigarin.

Ƴan ƙungiyar sun yi  kira ga gwamnatin tarayya ta kafa gidauniyar da za ta tallafa wa yaƙi da shan taba sigarin wadda tun a shekarar 2015 aka gabatar da wannan buƙatar amma bata samu sa hannu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply