Home Lafiya Yaɗuwar Covid-19 na ƙara munana a Nijeriya

Yaɗuwar Covid-19 na ƙara munana a Nijeriya

187
0

Ahmadu Rabe Yanduna

 

A Nijeriya an sake samun sabbin mutane 49 masu ɗauke da cutar Covid-19.

A wata sanarwa da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta fitar da misalin ƙarfe 10:40 na daren jiya a shafin intanet na cibiyar ta ce an samu waɗanda suka kamu da cutar daga jihohi 6.

Jihohin su ne; Lagos 23, Abuja 12, Kano 10, Ogun, Oyo da Ekiti kowanen su guda ɗaya.

Daga karfe 10:40 na daren ranar 18 ga Afrilu akwai adadin masu ɗauke da cutar a Nijeriya ya kai 542.

Haka an sallami mutum 166 da suka warke yayin da mutum 19 suka mutu.

Ga kuma yadda adadin masu ɗauke da wannan cuta na kowacce jiha tun daga lokacin da cutar ta bulla a Nijeriya;

Lagos- 306
FCT- 81
Kano- 37
Osun- 20
Oyo- 16
Edo- 15
Ogun- 12
Kwara- 9
Katsina- 9
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 6
Delta- 4
Ekiti- 4
Ondo- 3
Enugu- 2
Rivers-2
Niger- 2
Benue- 1
Anambra- 1

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply