Home Labarai Ya bugi matarsa har ta mutu a ranar Kirsimeti

Ya bugi matarsa har ta mutu a ranar Kirsimeti

91
0

Abdullahi Garba Jani

Rundunar ‘yansanda jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 37 mai suna Mutiu Sonola bisa zargin ya bugi matarsa mai shekaru 34 har ta mutu a ranar Kirsimeti.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan a cikin wata takarda, inda ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar da lamarin ya faru, bayan da mahaifinta ya kai rahoton kisan diyarsa ga ‘yansanda.

Ya ce mahaifin matar ya ba da labarin cewa an buga ma sa waya ana fada ma sa cewa akwai rashin jituwa tsakanin diyarsa da mijinta, inda har aka ce yana ta bugunta har abin ya fi karfinta.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan ya ci gaba yana cewa, mahaifin matar ya garzaya a gidan daga nan aka kwashe ta sai asibiti, inda likitoci suka tabbatar da ta mutu.

Ya ce tuni kwamishinan ‘yansanda na jihar ya ba da umurnin a mayar da wanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka don idasa binciken lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply