Home Labarai Ya daɓa wa matarsa wuƙa ta mutu

Ya daɓa wa matarsa wuƙa ta mutu

35
0

Wani mutum mai shekaru 46, ya shiga hannun jami’an rundunar ‘yansanda ta jihar Ogun bisa zargin dabawa matar shi wuka har lahira.

An kama Olatunji, ma’aikaci a karamar hukumar Remo ta arewa biyo bayan korafin da mahaifin marigayiyar, Alhaji Ambali Yinusa ya yi, wanda ya kai rahoto a shelkwatar rundunar ƴansanda reshen Owode-Egba cewa surukinsa Sobola Olatunji ya samu rashin fahimta da matarsa ​​Momudat Sobola wanda har ta kai su ga fadan ya yi tsamari.

Kakakin rundunar ‘yansanda na Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi a cikin wata sanarwa ya ce a cikin fadan da ake yi, wanda ake zargin ya dauki wuka inda ya soka wa matarsa ​​a gadan baya.

Bayan samun rahoton, DPO din na Owode-Egba, CSP Matthew Ediae ya umurci jami’an ƴansanda da su garzaya zuwa inda lamarin ya faru don kama wanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba, nan take kuma aka hanzarta da wadda aka azabtar zuwa asibiti don bata kulawar gaggawa, sai dai ana tsaka da mata magani ta ce ga garinku nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply