Home Labarai Ya damfari masu neman aikin-albashi Naira Milyan 1.3

Ya damfari masu neman aikin-albashi Naira Milyan 1.3

69
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”am2egccj1″ data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”vec4u8q22q” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”9ns9mvwztw” animation_delay=”0″]

Wani ma’aikaci mai suna Nelly Kalu wanda ake zargin ya damfari masu neman aikin albashi su 5 Naira Milyan 1da dubu 300 ya gurfana a gaban kotun majistare da ke Ikaje, Lagas a safiyar Litinin din nan.

 

Yan sanda sun gurfanar da shi inda suke tuhumarsa da aikata laifuka guda shida. Wasu daga cikin laifukan su ne sata da samun kudi ta hanyar damfara.

Mai gabatar da kara Segeant Adetutu Sanusi ce ta sanar da haka. Ta ce Mr. Nelly ya damfari : Mr Temitayo Olorunsola, Friday Agada, Oluwaseun Adeshola, Babatunde Ayoola da kuma Henry Agboge ta hanyar yi musu alkawarin zai samar musu aiki a kamfanin sarrafa fulawa na Honeywell Flower Mill duk da cewa ya san ba zai iya samar musu ba.

 

Yar sandar ta shaida wa kotu cewa Mr. Nelly ya aikata laifin a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019. Ya kuma yi amfani da dabaru kala kala wurin karbar kudade daga wurin masu neman aiki duk da cewa ya san ba zai iya samar musu ba.

 

Sai dai kuma shi Mr Nelly ya musanta duk zarge zargen da aka yi masa.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN, ya ce irin wadannan laifuka da ake zarginsa da shi, za su iya jefa mutum a gidan yari. Aikata laifin sata a bisa doka a jihar Legas na da hukuncin daurin shekaru 3, yayinda samun kudade ta hanyar damfara ke da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15.

 

Alkalin kotun justice Emeka Opara ta bayar da belin wanda ake zargi inda ta bukaci a sake dawowa kotu a ranar 30 ga watan Oktoba don ci gaba da shari’ar.

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply