Home Labarai Ya gudu ya bar jaririnsa a kan Naira 220,000

Ya gudu ya bar jaririnsa a kan Naira 220,000

153
0

Makonni biyu ke nan, bayan da wani uba mai suna Austin, ya gudu ya bar matarsa da jaririn da ta haifa a wani asibitin kudi a Legas don ba ya da kudin biyan aikin da aka yi wa matar Naira 220,000.

Matar mai suna Halimat ta ce ta haifi jaririnta namiji a ranar 25 ga watan jiya na Juli ta hanyar yi ma ta aiki, kuma tun daga nan, ba ta kara saka mijinta a ido ba, ita kuma ba ta da kudin da za ta biya.

Halimat da ke sayar da gasasshen nama da kifi, ta ce ‘yan kudaden da ta ke samu ba su iya isarta ta biya kudin wannan aiki, kuma ga sauran yara tana ciyarwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply