Home Labarai Ya kamata a hana Fulani zuwa da shanu kudancin Nijeriya – Ganduje

Ya kamata a hana Fulani zuwa da shanu kudancin Nijeriya – Ganduje

48
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci da a kirkiri dokar da za ta hana makiyaya tafiya da shanu daga Arewa zuwa wasu yankuna a kasar nan don dakile rikicin manoma da makiyaya.

Ya yi wannan kira ne a garin Daura ta jihar Katsina a ranar Asabar yayin zantawa da manema labarai.

Gwamnan ya ce rikicin manoma da makiyaya ba zai zama tarihi a kasar nan ba, har sai anyi dokar hana tafiya da shanu daga yankunan Arewa zuwa Kudancin kasar.

Ganduje ya bayyana irin nasarar da gwamnatinsa ta samu a jihar Kano kan dakile rikicin manoma da makiyaya da ma ta’addanci baki daya sakamakon hana makiyaya yawo da shanu ta hanyar samar musu da rugage.

“Yanzu haka mun gina gidaje ga makiyayan, mun samar da dam da kuma asibitin dabbobi don inganta rayuwarsu, da hakan ne muka yaki duk wani rikici ko ta’addanci a fadin jihar” a cewarshi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply