Home Labarai Ya kamata FG da ASUU su mayar da wuka kube –...

Ya kamata FG da ASUU su mayar da wuka kube – Ahmad Lawan

191
0

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya roki gwamnatin tarayya da mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su mayar da wukakensu cikin kube, don kawo karshen yajin aikin da kungiyar ASUU din ke yi domin bai wa daliban damar komawa. zuwa aji.

Sanata Lawan ya yi wannan rokon ne a ranar Litinin ya yin ganawa da mambobin kungiyar ASUU a majalisar kasa, inda ya ce rashin cimma matsaya ba zai haifar wa da kasar na da mai ido ba.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce kungiyar ta shigar da korafi game da tilasta shigar da membobinta shiga tsarin nan na biyan albashin bai daya (IPPIS) da gwamnatin Nijeriya ta yi da ma sauran korafe-korafe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply