Shugaban majalisar wakilan Nijeriya Femi Gbajabiamila da ke jagorancin sasanta rikicin ‘yan kasuwa a kasar Ghana, ya bukaci hukumomin kasar da su sake yin nazarin dokar nan da ta ce dole sai mutum yana da jarin Dala milyan 1 kafin ya fara gudanar da kasuwanci a kasar.
Gbajabiamila ya bayar da shawarwarin da za su taimaka wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa ‘yan Nijeriya da ke harkokin kasuwanci a Ghana.
Ya kuma ce ya kamata Nijeriya da Ghana su bi hanyoyin irin na diflomasiyya domin warware takaddamar cikin ruwan sanyi.
