Wani jigon jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya Adamu Garba ya yi kira ga babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta hana amfani da dandalin “twitter” a Nijeriya.
Dama dai, jigon jam’iyyar APCn ya taba caccakar shugaban dandalin Jack Dorsey bisa zargin kafa wani asusu da ake tallafa wa masu zanga-zangar kawo karshen ayyukan ‘yansandan SARS.
A wata kara da Adamu Garba ya shigar karkashin dokar ‘yancin dan’Adam, ya kuma bukaci mamallakin kamfanin na twitter da ya biya shi diyyar Dala milyan 1 bisa wannan asusu da ya kafa.
