Home Labarai Ya kashe mahaifiyarsa da yaransa biyu

Ya kashe mahaifiyarsa da yaransa biyu

140
0

Ƴan sanda a jihar Anambra sun kama wani mutum a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa bisa zargin kashe mahaifiyarsa mai shekara 85 da kuma yaransa biyu a ranar Alhamis.

Mutumin mai suna Emeka Ezimadu mai shekara 47, ya yi amfani da adda wajen kashe yaran nasa ƴan shekara 9 da shekara 2 da kuma mahaifiyarsa lokacin da suke bacci, sannan kuma ya raunata yara uku.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Haruna Muhammad ya ce jami’ai sun isa wurin da abun ya faru inda suka garzaya da su asibiti kuma a nan aka tabbatar da mutuwarsu.

Ƴan sanda sun ce wanda ake zargin ya shiga wani halin rayuwa ne da ya sanya shi yin ta’asar, a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply