Home Labarai Ya roki kotu da ta amso ma sa firij da tukwane daga...

Ya roki kotu da ta amso ma sa firij da tukwane daga hannun tsohuwar matarsa

76
0

Abdullahi Garba Jani

Wani dan kasuwa a Kaduna mai suna Muhammad ya roki kotun Majastare ta 2 da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna da ta karbo ma sa wasu kayan amfanin gida daga hannun tsohuwar mayarsa mai suna Umma.

Muhammad ya fada wa kotu cewa Umma ta tafi da firij, tukwane da “gas cooker dinsa bayan da suka rabu.

A nata bangare, wadda ake kara, Umma ta fada wa kotu cewa shi ya bata wadannan kayan a lokacin da tana amarya.

Alkalin kotun Malam Murtala Nasir, ya tambayi Muhammad ko yana da shaida, amma ya ce babu.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ba da labarin cewa an fara sauraren karar ne a ranar 18 ga watan jiya na Nuwamba.

Alkalin kotun ya umurci Umma da ake kara da ta gabatar da dukkanin kayan da aka lissafo a gaban kotun a ranar 10 ga wannan wata na Disamba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply