Home Labarai Ya zama wajibi mu hada kai muddin muna son yakar ta’addanci in...

Ya zama wajibi mu hada kai muddin muna son yakar ta’addanci in ji Gwamna Masari

83
0

Abdullahi Garba Jani

Gwamnan jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari ya kara nanata kudirin gwamanatinsa na lalubo duk hanyoyin da suka dace don tunkarar matsalolin tsaro a jihar.

Gwamna Masaei na magana ne a lokacin da ya gana da mambovin kungiyar gamayyar jam’iyyu ta jihar a Katsina.

Gwamnan ya ce ya zama wajibi sai an hada kai muddin ana so a samu hanyoyin warware matsalolin da ke ci wa jihar tuwo a kwarya.

Ya ce batun karancin tsaro na da bukatar a ajiye duk wani bambancin siyasa, inda ya bukaci mambobin kungiyar da su ba da shawarwarin da suke ganin sun dace son ceto jihar da al’ummarta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply