Home Labarai Ku guji yada labaran karya, Rundunar sojin Nijeriya ta ja kunne

Ku guji yada labaran karya, Rundunar sojin Nijeriya ta ja kunne

89
0

Ma’awiyya Abubakar Sadiq

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana illa da matukar hadarin amfani da kafafen sadarwar zamani wajen yada labaran karya wadanda ta bayyana cewar yana kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron kasa.

Shugaban Sashen Huldar Sojoji da Farar Hula na rundunar soji, Manjo Janar US Muhammad ne ya bayyana hakan a wajen taron tattaunawa da ma’abota amfani da kafafen Sadarwar Zamani da ‘Yan Jaridun Yanar Gizo kusan 300 a ranar Litinin a Sakkwato.

Ya ce taron wanda aka fara gudanarwa a 2018 a birnin Patakwal na jihar Ribas, na da manufar tattaunawa tsakanin sojoji da fararen hula domin samar da hadin kai da fahimtar juna.

Yace ba shakka wannan taron zai kara ba mu damar da ta kamata ta tattaunawa kai tsaye da musayar ra’ayoyi, domin magance matsalolin yada labaran karya da ya yawaita a kafafen sadarwar zamani.” Ya bayyana.

Ya ce a na tsammanin taron wanda aka gudanar tare da hadin guiwar Security Affairs Limited ya wayar da kan mahalarta kan nasarorin da aka samu a Rundunar Sojoji ganin cewar an samu ci gaba sosai a karkashin sashen huldar sojoji da farar hula tun kirkiro da sashen a 2010.

A jawabinsa Mashawarci na Musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato kan Ayyuka na Musamman, Dahiru Yusuf Yabo ya bayyana taron a matsayin muhimmi bisa ga abubuwan da aka tattauna.

Ya bayyana cewa masu amfani da kafafen sadarwar zamani suna da tasiri kwarai wajen canza halayen mutane, don haka ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da wannan damar wajen taimakawa jami’an tsaro.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply