Rahotanni na cewa an ƴan wasan ƙasar Gabon ciki harda jagoran ƴan wasan Arsenal Pierre Emerick Aubameyang sun kwana a kan daɓen filin jirgi a Gambia.
Ƴan wasan dai sun je ƙasar ne domin buga wasan neman shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika, wanda Gabon ta yi rashin nasarar shiga a shekarar 2019.
Saidai kuma hotunan da ke yawo a Twitter sun nuna yadda aka bar ƴan wasan kwance a daɓen filin jirgin tun misalin ƙarfe 11 na daren jiya agogon ƙasar.
