Home Labarai Yadda Buhari ya jagoranci ƙarƙare bikin ranar sojoji

Yadda Buhari ya jagoranci ƙarƙare bikin ranar sojoji

44
0

A ranar Juma’ar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci manyan jami’an gwamnati da wakilan diflomasiyya don tunawa da sojojin kasar da suka sadaukar da rayuwarsu.

 

Bikin na yau dai, shi ne na karshe a bukukuwan da akai na tunawa da sojoji na shekarar 2021 da aka fara a karshen shekarar da ta gabata.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da Babban Alkalin Nijeriya Tanko Muhammad ne suka jagoranci manyan hafsoshin tsaron kasar a wajen nuna girmamawa ga sojojin da aka yi a Abuja.

Baya ga girmamawar da aka yi wa mazan famar, an kuma gudanar da addu’o’i ga dakarun kasar da suka mutu da wadanda ke raye, yin shiru na minti guda, sakin tantabara don nuna zaman lafiya da kuma sanya hannu ga rajistar wadanda suka halarci taron da dai sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply