Home Labarai Yadda direba ya gano wanda suka sace shi a cikin fasinjojinsa

Yadda direba ya gano wanda suka sace shi a cikin fasinjojinsa

174
0

Takaddama ta barke a tashar motar Kwannawa dake karamar hukumar Dange-Shuni a jihar Sokoto, bayan da wani direban mota ya gane daya daga cikin masu satar mutane da suka sace shi a cikin fasinjojinsa.

Direban da aka sakaya sunansa, an sace shi akan hanyar Kankara dake cikin jihar Katsina yayin da yake dawowa daga Kano wata 2 da suka shude kuma ya yi sati ukku tsare a hannun masu satar mutanen har lokacin da aka biya kudin fansa sannan suka sake shi.

Al’amarin ya farune a ranar Lahadi, lokacin da direban ya gane mai satar mutanen bayan shigarsa motarsa da niyyar zuwa Kano, ya kuma hanzarta sanar da ma’aikatan tashar motar aka kai rahoto zuwa ofishin ƴansanda.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Sokoto DSP Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun tsare motar bayan fitowarta daga tashar suka fito da wanda ake zargi zuwa shelikwatarsu da ke garin Sokoto ya kuma amsa laifinsa bayan tuhumarsa, yanzu haka suna ci gaba da bincike kan lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply