Home Labarai BIDIYO: Yadda muka ceto ƴan Nijar da ƴanbindiga suka sace – Masari

BIDIYO: Yadda muka ceto ƴan Nijar da ƴanbindiga suka sace – Masari

118
0

Gwamnatin jihar Katsina ta ceto wasu mutane 9 ‘yan kasar Nijar da ‘yanbindiga suka yi garkuwa da su.

Wadanda aka ceton, da suka hada da mata hudu maza hudu sai jinjiri guda, sun ce an sace su ne a kauyensu na Bima da ke cikin Maradin jamhuriyar Nijar, kwana 9 da suka wuce.

Da yake magana da ‘yanjarida, a gidan gwamnatin jira, lokacin da yake karbar kubutattun, Gwamna Aminu Bello Masari na Katsina, ya ce an yi nasarar kubutar da mutanen ne a kokarin da gwamnatinsa hadin guiwa da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi.

Masari ya ce har yanzu gwamnatinsa ba ta yin wata tattaunawa da ‘yanbindigar, saidai ta ci gaba da bin hanyar da ta bi ne wajen ceto ‘yan makarantar sakandiren Kankara da aka sace.

Daya daga cikin kubutattun Issofou Ali, ya ce su goma ne aka sace daga kauyen, saidai an saki dayar wadda ‘yar Nijeriya ce bayan ta biya kudin fansa, yayin da su kuma aka daure su a cikin daji tsawon kwana tara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply