Home Sabon Labari Yadda Sanata Kaita da Hon. Kusada suka zarce sa’anninsu ‘yan majalisa

Yadda Sanata Kaita da Hon. Kusada suka zarce sa’anninsu ‘yan majalisa

452
0

Ra’ayin Imrana Daura

 

Sanata Ahmed Babba Kaita da Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada wasu Yan-Majalissun tarayya ne guda biyu da suka fito daga jihar Katsina. Dukkansu sun fito ne daga mazaba daya ta Majalissar Tarayya, sannan kuma sun fito ne daga yanki daya na Majalissar Dattawa wato Yankin Katsina ta Arewa (Daura Zone).
Koda baka tare da su a siyasance, dole ne ka yadda cewa mutanen nan mutanen kirki ne, suna da kirki, kuma suna safke nauyin da al’umma ta dora masu. Ko shakku babu sun fi sauran ‘yan majalissu dangantaka da mazabunsu, sunfi sauran ‘yan majalissu kawo ma mazabunsu ci gaba wajen gina rayuwar matasa, sun fi nuna biyayya ga jam’iyya fiye da kowane danmajalissa.

Sanata Ahmed Babba Kaita shi ne ke shugabantar kwamitin Majalissar Dattawa na Asusun Tallafa ma makarantun gaba da sakandire na Gwamnatin Tarayya. Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada kuma shi ne ke shugabantar Kwamitin Majalissar Wakilai na Hukumar Raba Dai-Dai ta Kasa.
A kasa da shekara biyu da suka shafe a Majalissa, sun samar wa matasan Kankia/Kusada/Ingawa (Bangaren Rt. Hon. Kusada) da kuma Yankin Majalissar Dattawa ta Daura Zone (Sanata Babba Kaita) akalla mutum 500 aikinyi.

Imrana Daura
Imrana Daura

A Jihar Katsina, kashi 40 cikin 100 na ayyuka da matasa suka samu a Gwamnatin Tarayya ya fito ta hanyar wadannan mutanen biyu.
Ina kira ga kungiyoyin matasan jihar Katsina, kungiyoyin siyasa, da kungiyoyin ci gaba na jihar Katsina su nemo wata hanya mafi kyau da za a karrama wadannan bayin Allah.

Zan dakata anan da kira da jawo hankalin matasanmu masu son cigaba da su fara nemo hanyar shirya wannan gagarumin taron karramawa.

Musamman:
Muhammad Aminu Kabir
Abu S. Aminu
Ado Umar Lalu
Shamsuddeen Dahiru Mani
Al-Ameen Batsari
Mubarak G Isa Mani
Faruq D Fago
Mubarak Mamuda Rimi
Lawal Shunku Adamu
Hamisu Mogal Daura
Abubakar Kafin Soli
Bello Sukuntuni
Babangida Alolo Yandoma
Musa Nuhu Kankia
Ahmad A Daura
Yulaks KY
Da dai sauransu.

Ni ne Imrana Daura, marubuci, mai ra’ayin kare muradin mulkin dimukuradiyya. Za a iya samu na a imrana0012@gmail.com

 

Na gode.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply