Home Labarai Yadda wani mutum ya mutu a kokarin ceto tinkiya daga rijiya

Yadda wani mutum ya mutu a kokarin ceto tinkiya daga rijiya

136
0

A ranar Talatar da ta gabata ne, wani abin tu’ajibi ya faru a unguwar Sha’iskawa cikin karamar hukumar Dambatta jihar Kano, a lokacin da wani mutum mai suna Abdulhamid Muhammad ya mutu a lokacin da ya ke kokarin ceto wata tinkiya da ta fada rijiya.

Jaridar Daily Trust da ta ziyarci gidan mamacin, ta gano cewa matarsa da tinkiyar da sauran ababen bukata duk an mayar da su garin Moriki, mahaifarsa cikin jihar Zamfara.

Malam Abdulhamid da ya haura shekaru 40, ya fada rijiyar mai gaba 35 da ake amfani da ita wajen samun ruwa sha.

Malama Jamila, mata ce da ke zaune gida daya da mamacin, na daga cikin tsirarun mutanen da suka shaidi wannan lamari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply