Home Sabon Labari “Yadda ‘yan bindiga suka addabe mu a Karamar Hukumar Rogo jihar Kano”

“Yadda ‘yan bindiga suka addabe mu a Karamar Hukumar Rogo jihar Kano”

464
0
Ba wai baƙon abu bane a fito a gaya wa duniya irin matsalar tsaron da wannan ƙaramar hukuma tamu ke fuskanta ba, wanda kuma hakan barazana ce babba ba ma ga iya ƙaramar hukumar ba har da maƙwabta da ma jihar Kanon baki daya.
Duk mutumin da ke rayuwa a Ƙaramar hukumar Rogo ya kwana ya tashi da sanin yadda masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa suka fara faɗowa yankin namu da fara zama barazana kowa ya san yadda wadannan mutane suka yi garkuwa da:
*Matar ɗan gidan Alh Isah kafinta falgore
*An ɗauke dagacin garin Karshi wanda sai da aka biya kuɗin fansa
*An kuma ɗauke matar dagacin garin Tsara wanda shima labarin ya zaga ko ina
*A wannan satin kuma da muke ciki masu garkuwa da mutane sun kuma shigowa garin Falgore inda suka ɗauke mata da ɗan da ta haifa sannan kuma suka yi nasarar harbe direban ƴan sintiri gami da ƙona motar yan sintirin baki ɗaya.
Ƙaramar hukumar Rogo dai nada iyaka da jahohin Kaduna da Katsina wanda kuma wannan jihohi na fama da matsalar tsaro. Duk da ƴan sanda na ƙaramar hukumar Rogo na bakin ƙoƙarinsu na ganin sun kare lafiya da dukiyar jama’a a wannan yanki amma abun na neman yafi ƙarfinsu, aikin ya wuce ace su kaɗai za suyi dole sai al’umma sun fito sun bada gudunmawa a yankin da suke domin kare kansu, iyalinsu da kuma dukiyarsu.
A zahirin gaskiya wannan fitana da ta kunno kai ba ƙarama bace domin mutanen da suke wannan garkuwa da mutane ba a san ko su waye ba ba a san a ina suke ba, kuma Hausawa na fadin sai da dan gari a kan ci gari.
Ghali Nasiru Rogo mawallafin wannan rubutun
Muna mai miƙa kira na kai tsaye ga wannan mutane kamar haka:
Na farko gwamnatin jihar Kano da ta fito ta bayar da duk gudunmawar da ta dace na ganin an kawo ƙarshen wannan matsala, ƙin ɗaukar wannan matakin kuwa barazana ce ga jihar Kanon baki ɗaya domin kuwa da can wasu wurare masu nisa muke ji amma yau gashi a tare damu.
Sannan gwamnatin Karamar hukumar Rogo ita kuma ta samar da ƙungiya ta musamman ko kuma ta ƙara wa ƙungiyar ƴan sintiri ƙarfi wajen biyan su haƙƙinsu da kuma ba su kayan aiki masu nagarta domin su ma suna da gudunmawar da za su iya badawa.
Manyan attajirai, ƴan kasuwa, ƴan siyasa, da manyan manoma da sauran masoya na wannan yanki ku bayar da dukiyarku wajen addu’a da kuma samar da tsaro domin kune ku ka fi kusa da barazana ga wannan mutane.
Malamai da sauran al’ummar wannan yanki ya zama wajibi mu mayar da hankali wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da dawwamar kwanciyar hankali ba dare ba rana, malamai ku hau mambarin Juma’a da majalisai na karatu ku yi wayar da kan jama’a tare da yin addu’oi.
Abu na ƙarshe mutanen kowanne gari na wannan yanki ku bayyana dukkanin motsin abin da ba ku yarda da shi ba ga hukumar ƴan sanda a yankinku, sannan kuma ku zama jami’an tsaro na kanku a kodayaushe.
Muna adduar Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu. Allah ka karemu ka tsare dukiyar mu da lafiyar mu. Allah ka dauke wannan fitina da bala’i a doron kasa. Ya Allah ka shiryi shuwagabannin mu.

 

Daga alƙalamin

Ghali Nasiru Rogo

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply