Home Labarai Yajin Aiki: ASUU ta ja daga da gwamnatin Sokoto Kungiyar

Yajin Aiki: ASUU ta ja daga da gwamnatin Sokoto Kungiyar

196
0

Ƙungiyar Malamman Jami’o’i reshen Jami’ar jihar Sakkwato sun yi biris da umurnin da gwamnatin jihar ta bayar na sake buɗe makarantu.

Shugaban ƙungiyar Dr. Attahiru Sifawa wanda ya bayyana haka a wata zanta wa da ƴan jarida a Sakkwato, ya kuma gargaɗi ƴaƴan ƙungiyar kan koma wa aikin.

Ɗalibai da dama sun nuna rashin jin daɗi kan wannan mataki da ƙungiyar ASUU reshen Jami’ar ta ɗauka duk da cewa gwamantin jihar ta ce a dawo makaranta a ranar 12 ga wannan wata, amma kuma batare da dakatar da yajin aikin ba.

Kwamishinan Ilimi mai zurfi na jihar Farfesa Bashir ya ce yana fatar cimma matsaya kan yajin aikin, saidai kuma haƙa bata cimma ruwa ba, a zaman da suka yi na ranar Laraba da shugabannin ƙungiyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply