Home Labarai Yajin aiki: FG za ta zauna da shugabannin SSANU da NASU

Yajin aiki: FG za ta zauna da shugabannin SSANU da NASU

33
0

Wakilan Gwamnatin Tarayya za su zauna da shugabannin kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya (SSANU) da kungiyar ma’aikatan jami’o’in (NASU) a ranar Talatar nan don tattauna batun shirin tafiya yajin aikin da kungiyoyin ke yi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Ministan kwadago Christ Ngige zai shugabanci wakilan gwamnati yayin da shugaban kungiyar SSANU Mohammed Ibrahim Haruna zai shugabanci kungiyoyin yayin zaman ganawar.

A kwanakin baya ne dai hadakar kungiyoyin biyu suka yi barazanar tsunduma yajin aiki daga ranar Juma’a 5 ga watan Fubrairun nan da muke ciki bisa zargin rashin adalci dangane da kasafin kudin da gwamnatin tarayya ta ba jami’o’i har Naira bilyan ₦40bn.

Sauran abubuwan da suka jawo tada kayar bayan sun hada da rashin biyan ariyas na mafi karancin albashi, rashin aminta da tsarin biyan albashin IPPIS, rashin cika yarjejeniyar gwamnati da ƙungiyoyin ta shekarar 2009 da rashin biyan hakkokin ƴan ƙungiyar da suka ajiye aiki.

A cikin takardar gayyata da ministan ya aikewa majiyar DCL Hausa a daren jiya Litinin ta hannun kakakin Ma’aikatar Ƙwadagon Charles Akpan ya bayyana cewa gwamnatin ta shirya zaman ne don ganin an warware matsalolin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply