Home Labarai Yajin aiki: Kotu ta taka wa kungiyoyin kwadago birki

Yajin aiki: Kotu ta taka wa kungiyoyin kwadago birki

157
0

Kotun sasancin ma’aikata ta kasa ta dakatar da kungiyar kwadago ta kasa NLC da gamayyar kungiyoyin kwadago TUC da ma sauran kungiyoyi masu alaka da su, da su dakatar da yajin aikin da su ke shirin farawa daga ranar Litinin.

Mai shari’a Ibrahim Galadima ya ce kotun ta bayar da wannan umurni ne har sai an yanke hukuncin karar da wata kungiya ta shigar da ta ke kalubantar yajin aikin da kungiyoyin suke shirin yi.

Kotun ta kuma umurci shugaban ‘yansanda da kuma shugaban hukumar tsaron ciki DSS da su bayar da kariya ga ma’aikata yayin da suke gudanar da halartattun ayyukansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply