Home Labarai Yajin Aiki: Majalisar wakilai ta gayyaci ASUU

Yajin Aiki: Majalisar wakilai ta gayyaci ASUU

64
0

Majalisar wakilan Nijeriya ta gayyaci kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU da ma’aikatar ilimi da ta kwadago, kan yajin aikin gargadi da kungiyar ta shiga.

Wannan na daga cikin matakan da majalisar ta dauka a kudirin da ke bukatar gaggawa dad an majalisa Dachung Bagos ya gabatar a zaman majalisar na yau Talata.

Bagos ya ce akwai bukatar gaggawa ga majalisar ta shiga tsakanin rikicin da gwamnatin tarayya ke yi da ASUU kan sabon tsarin biyan kudi da tattara bayanan ma’aikata, da dai sauran matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu.

Sauran ‘yan majalisar sun koka da cewa idan har ba a yi kokarin magance matsalolin ba, kungiyar za ta fada yajin aikin sai baba ta gani a karshen yajin aikin na gargadi da suke yi.

Sun kuma bayyana yajin aikin a matsayin cin fuska ga kasa, tare da cewa a ko yaushe matsalar yajin aikin kan dalibai take karewa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply