Home Labarai Yajin aiki ya fusata ɗaliban Nijeriya a Twitter

Yajin aiki ya fusata ɗaliban Nijeriya a Twitter

79
0

Bayan shafe lokaci mai tsawo a na yajin aiki sanadiyyar ja-in-ja tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i a Nijeriya, daliban jami’o’in na ci gaba da kokawa kan halin da rashin jituwar ya jefa su.

Ɗaliban jami’o’in ƙasar na ci gaba da bayyana damuwa game da kiran da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi wa ɗaliban cewa su nemi wata hanyar dogaro da kai.

Matakin dai ya biyo bayan zargin da ƙungiyar ASUU ta yi wa gwamnati, na nuna halin ko-in-kula wajen biyan buƙatunsu, da kuma dakatar da biyansu albashi tsawon wata takwas.

A kan haka ta dauki matakin sanar da daliban jami’o’i cewa su cire rai da komawa makaranta yanzu, wanda ya janyo suka kwashe wata takwas suna zaman dabaro a gida.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply