Mawakiya Simi, ta yi Allah wadai ga shugabannin Nijeriya kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ke yi.
ASUU ta shiga ya jin aiki tun a watan Maris, kuma har yanzu sun kasa cimma matsaya tsakaninsu da gwamnati.
Rashin samo daidaito tsakanin bangarorin biyu dai ya janyo tsayawar karatu a tsakanin daliban kasar, wadanda yajin aikin ya fi yi wa illa.
Da take Magana a shafinta na Twitter Simi, ta nuna bacin ranta kan makomar karatun talakawa ‘yan Nigreia, sannan ta yi kira ga shugabannin Nijeriya su dauki matakin da ya dace.
A cewarta gwamnati bata nuna damuwa kan buri da makomar matasan Nijeriya da ke karatu a jami’o’in kasar.
