Home Labarai Yaki da ta’addanci: MURIC ta jinjinawa rundunar ‘yan sandan Nijeriya

Yaki da ta’addanci: MURIC ta jinjinawa rundunar ‘yan sandan Nijeriya

90
0

Kungiyar kare ‘yancin Musulmi ta Nijeriya MURIC ta yi kira ga rundunar ‘yan sandan kasar da ta ci gaba da kokarin da take na fatattakar ‘yan ta’adda a maboyar su, bayan nasarar da ta samu na fatattakar su a dajin Kuduru da ke jihar Kaduna, inda aka kashe kimanin ‘yan ta’adda 250.

Daraktan kungiyar Farfesa Ishaq Akintola wanda ya yi wannan kira a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan ta’addan sun takurawa rayuwar jama’ar yankin, kafin ‘yan sandan su dauki wannann mataki.

Ya ce MURIC ta yi amanna da wannann kokari na ‘yan sanda da kungiyar ta ce ya sanya ‘yan ta’addar sun dandana kudar su tare da gane shayi ruwa ne.

Ya kara da cewa ko a baya, kungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaron kasar su farmaki maboyar ‘yann ta’addan domin ta haka ne za a iya kakkabe su.

Haka kuma ya yabawa kokarin Babban Sufeton ‘yan sandan kasar Muhammad Adamu, kan tura wata tawagar ‘yan sanda domin jajantawa tare da duba jami’an da suka samu raunika a lokacin harin.

Sannan kuma ya yi kira gare shi, da ya dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa an biya iyalan ‘yan sanda biyu da suka rasa rayukan su diyya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply