Home Kasashen Ketare ‘Yan adawa sun kalubalanci yadda ake shirin zabe a Nijar

‘Yan adawa sun kalubalanci yadda ake shirin zabe a Nijar

158
0

Gamayyar jam’iyyu adawar jamhuriyar Nijar sun sake jaddada kalubalantar tsarin shirye-shiryen zaben kasar.

A cikin sanarwar ‘yan adawar bayan sun tabo batun sakamakon zaman majalisar sasanta jam’iyyun siyasar Nijar cewa da CNDP sun kuma bukaci da a aiwatar da ababe hudu (4) kamar haka :

Yin zaben kananan hukumomi kafin na shugaban kasa.

Ba ma ‘yan Nijar da ke ketare damar yin zabe.

Rushe hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta CENI

Murabus din mambobin kotun kundi tsarin mulkin

A karshe ‘yan adawar sun yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasar da ma sauran al’ummar da su ba da goyon bayansu don ganin an gudanar da sahihin zabe a kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply