Sama da mutane 200, ‘ya’yan jam’iyyar APC suka koma jam’iyyar PDP a karamar hukumar Kuje da ke Abuja.
Shugaban jam’iyyar PDP na yankin Kuje Alhaji Mohammed Ismaila ne ya amshe su a sakayariyar karamar hukumar.
Wadanda suka sauya shekar sun hannanta katinsu na zama jam’iyyar APC da tsintsiyoyi da fastoci, inda suka maye gurbimsu da na PDP.
Shugaban tawagar da suka sauya shekar, Mohammed Gambo, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewa ba su gamsu da tsarin APC bane, shi ya sa suka fita.
