Home Labarai ‘Yan bindiga sun saci dalibai 829 cikin shekaru 6 a Nijeriya –...

‘Yan bindiga sun saci dalibai 829 cikin shekaru 6 a Nijeriya – Bincike

143
0

Sakamakon yadda ta’addanci da satar al’umma ya zama ruwan dare, makarantu a fadin tarayyar Najeriya suka zama wurin harin ‘yanta’adda inda suka yi awon-gaba da daruruwan dalibai. Binciken jaridar Daily Trust ya bankado yawan daliban da aka sace tun daga shekarar 2014 zuwa wannan shekarar da kuma illar da hakan ta haifar ga tsarin koyarwa.

Alkalumma sun nuna cewa akalla daliban sakandire sama da 829 ne ‘yan bindiga da kungiyar Boko Haram suka sace a cikin shekara 6.

Adai-dai lokacin da sace daliban Kankara su 344 ya ja hankalin duniya baki daya wanda aka samu damar karbo su kwana 6 bayan batansu, har yau, sama da ‘yan mata 100 na Chibok na hannun ‘yan Boko Haram.

DCL Hausa ta labarta cewa satar daliban da ta zama ruwan dare musamman a arewa musamman Yobe, Katsina, Kaduna, Zamfara da sauransu ya sa jihohin suka rufe makarantunsu wanda hakan ke taimakawa wurin mayar da harkar ilimi a baya musamman a arewacin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply