Home Sabon Labari ‘Yan bindiga 300 sun kai hari a Katsina a lokaci daya

‘Yan bindiga 300 sun kai hari a Katsina a lokaci daya

128
0

Yan ta’adda akalla 300 sun kai hari a wasu kauyuka na kananan hukumomin Dutsin Ma da Dan Musa da Safana a jihar Katsina. Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ce ta sanar da haka a wannan Lahadi kamar yadda Kakinta SP Gambo Isah ya shaida wa gidan rediyon DW.

Lamarin dai ya faru ne a daren ranar Lahadi. An kuma samu alkaluma masu cin karo da juna a kan adadin mutanen da aka kashe. ‘Yan sanda sun ce mutum 33 ne suka rasa rayukansu amma wani mazaunin yankin da abin ya faru ya ce sama da mutum 70 ne ‘yan bindiga suka hallaka.

Jihar Katsina dai na ci gaba da fuskantar irin wadannan hare hare a yankunan karkara, galibi a tsakanin fulani makiyaya da manoma ko kuma ‘yan banga.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply