Home Sabon Labari ‘Yan bindiga na neman kudin fansa milyan N100 kafin su sako ‘yansanda

‘Yan bindiga na neman kudin fansa milyan N100 kafin su sako ‘yansanda

91
0

‘Yan bindigar da ke rike da ‘yansanda masu mukamin anini su 6 sun nemi da a ba su kudin fansa milyan 100 kafin su sako su.

‘Yansandan dai sun kwashe sama da mako daya bayan da aka yi garkuwa da su kan hanyar Zamfara-Katsina.

Punch ta rawaito cewa ‘yansandan na daga cikin wadanda ba da dadewa ba suka samu karin girma da ke aiki da “Mobile Squadron 6”, Maiduguri jihar Borno.

Bayanai sun ce an tura su aiki ne a jihar Zamfara a lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton-bauna a yankin Dogon Daji na jihar Katsina.

Punch ta gano cewa iyalan ‘yansandan sun fara yunkurin tattara Naira milyan 3 da kowane zai ba da dubu 5 domin a sako musu mazaje.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply