Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta sanar da mutuwar mutum daya bayan wani harin kwanton-bauna da ‘yanbindiga suka kai wa tawagar jami’an gwamnatin jihar.
A cikin wata takarda daga mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Muhammad Shehu, ta ce tawagar jami’an gwamnatin su na kan hanyar su ta komawa birnin Gusau daga Katsina, bayan sun kai wasu mata 26 da aka ceto daga hannun ‘yqn bindiga.
Takardar ta ce lamarin ya faru ne a Dogon Karfe, Gidan Jaja kan hanyar Jibia zuwa Zurmi.
Tawagar dai na karkashin jahorancin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Abubakar Mohammed.
