Home Sabon Labari ”Yan bindiga sun fara iko da wasu yankuna a Sokoto”

”Yan bindiga sun fara iko da wasu yankuna a Sokoto”

347
0

Mazauna yankunan karkara da ke yankin gabashin Sakkwato da ke fama da matsalar rashin tsaro na kokawa kan yadda ‘yan bindiga ke gudanar iko a yankunansu.

Wani da DCL Hausa ta zanta dashi ta wayar tarho ya bayyana yadda ‘yan bindiga ke gudanar da mulki a gabashin na Sakkwato. Ya yi zargin cewa ko jami’an tsaro ba sa iya zuwa yankin.

Kazalika wasu mazauna yankunan sun ce ‘yan bindiga na gudanar shari’o’i da kuma hukunta mutane iya yadda suke so, sun yi zargin cewa  ‘yan bindigar kan azawa mutane kudi idan anyi wani abu da suke gani a wajen su laifi ne.

To sai dai Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ASP Muhammad Sadiq Abubakar ya musanta zancen.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply