Home Sabon Labari Yan bindiga sun hallaka ƴan sanda biyu tare da garkuwa da babban...

Yan bindiga sun hallaka ƴan sanda biyu tare da garkuwa da babban jami’in lafiya

139
0

Hannatu Mani Abu/Banye

 

Rundunar ƴan sanda a jihar Edo ta tabbatar da kisan jami’an ta guda biyu waɗanda ke kula da tsaron wani babban darakta,Silvanus Okogbeni da ke kula da asibitin koyarwa na Irrua a jihar Edon Nijeriya.

 

Kamfanin dillancin labaru na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wani wurin shakatawa na Ramat Park dake ƙaramar hukumar Ikpba-Okha na jihar a ranar Litinin da ta gabata akan hanyar su ta dawowa Benin.

Yan sandan Nijeriya na atisaye

Mai magana da yawun hukumar ƴan sanda ta jihar Edo Chidi Nwabuzor ya shaida wa NAN cewa ana zargin ƴan bindiga ne suka kashe jami’an biyu da wasu farar hula biyu da har yanzu ba a gane ko su waye ba. Bayan haka kuma sun yi  garkuwa da babban jami’in lafiyar.

 

Nwabuzor ya ce kawo yanzu ana ci gaba da bincike domin gano masu hannu a lamarin. Sai dai ɗaya daga cikin manyan jami’an kungiyar asibitocin koyarwa na jami’o’i, Emanuel Igiechi ya bayyana damuwar sa akan yawaitar rashin tsaro da ke ci gaba da ƙaruwa a ƙasar tare da yin kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen daƙile faruwar hakan a gaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply