Home Labarai ‘Yan bindiga sun hallaka shugaban ‘yan banga a Neja

‘Yan bindiga sun hallaka shugaban ‘yan banga a Neja

154
0

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun sake kai hari a kauyen Madaka da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja inda suka kashe mutane uku ciki har da kwamandan ‘yan banga a yankin, Ishaku Alhassan da dansa, Abdulhameed Ishaku.

Shugaban ma’aikatan shugaban karamar hukumar Rafi, Mohammed Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mutane uku sun mutu a ya yin harin.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kuma sace wani basarake na garin Madaki sannan suka tafi da kayan abinci da kayayyaki masu daraja.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply