Home Labarai ‘Yan bindiga sun kashe danjarida a Nasarawa

‘Yan bindiga sun kashe danjarida a Nasarawa

133
0

A daren Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kashe tsohon ma’aji na kungiyar ‘yanjarida reshen jihar Nasarawa Benjamin Ekom.

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun kashe Mr Benjamin ne a gidansa da ke kauyen Washo karamar hukumar Nasarawa-Eggon.

Shugabannin kungiyar ‘yanjarida na jihar sun bukaci jami’an tsaro da su gano tare da hukunta wadanda suka aikata wannan kisa.

A cikin wata takarda daga shugaba da sakataren kungiyar Salihu Alkali da Sunday John, ta bayyana kisan da cewa abin Allah-wadai ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply