Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani babban limamin kirista mai suna Kayode Ogunleye, inda suka jefar da gawarsa a wani daji a kan babbar hanyar Aramoko-Ijero-Ekiti da ke jihar Ekiti.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa an gano gawar faston, wanda kuma ma’aikaci ne a karamar hukumar Ekiti ta Yamma a Jihar Ekiti, a gonarsa da ke kusa da dajin.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Daya daga cikin mazauna yankin, da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana kisan na Ogunleye a matsayin ta’addanci, ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka yi wannan aika-aika.
